Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan bindiga sun hallaka mutane 9 a Birnin Gwari

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin barayi ne sun hallaka mutane 9, da raunata wasu da dama a lokacin da suka afka wa kauyen Kaguru da ke yankin Birnin Gwari a jihar Kaduna, da ke arewacin Najeriya.

Wasu 'yan bindiga da ba'a san ko su waye ba sun hallaka mutane 9 a Birnin Gwari.
Wasu 'yan bindiga da ba'a san ko su waye ba sun hallaka mutane 9 a Birnin Gwari. Information Nigeria
Talla

Wasu mutanen da dama ne suka arce cikin dazuka, yayin da wadansu ke gudun hijira a kauyukan da ke makwaftaka.

Isyaku B. Aliyu tsohon shugaban karamar hukumar, ya shaidawa Sashin Hausa na RFI cewa, maharan sun cinnawa gidaje da dama a kauyen wuta, har yanzu kuma ba’a gano wasu daga cikin mutanen da suka bace ba, bayan da suke tsere cikin daji.

Aliyu ya kara da cewa kwanaki goma da suka gabata, wasu ‘yan bindiga sun kai hari cikin dare kan kauyen Kirazu, a karamar hukumar ta Birnin Gwari, inda suka hallaka yaro daya da kuma jikkata wasu mutane da dama.

00:54

'Yan bindiga sun hallaka mutane 9 a Birnin Gwari

Nura Ado Suleiman

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.