Isa ga babban shafi
Najeriya

An kama 'yan Boko Haram a Zaria

Akalla Mutane 10 da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne da suka tsere daga dajin Sambisa aka cafke a garin Zaria da ke jihar Kaduna ta Najeriya.

Wasu daga cikin mayakan kungiyar Boko Haram a dajin Sambisa na Borno da ke Najeriya
Wasu daga cikin mayakan kungiyar Boko Haram a dajin Sambisa na Borno da ke Najeriya Youtube
Talla

Rahotanni sun ce, jami’an ‘yan sanda sun yi nasarar cafke mutanen ne a Dogarawa da ke sabon garin Zaria bayan sun samu bayanan sirri game da su.

Wani babban jami’in ‘yan sanda da ke kula da shiyar Zaria, Muhammad D. Shehu ya shaida wa manema labarai cewa, wasu mutane ne suka sanar da su take-taken mayakan, lamarin da ya sa aka tura ‘yan sandan sintiri kimanin 100, inda suka yi nasarar killace gidan da mayakan ke ciki.

Mr. Shehu ya ce, tuni aka tasa keyar mayakan zuwa shalkwatan ‘yan sandan, yayin da binciken farko ya nuna cewa, mutanen sun yi hijira ne daga Darul Islam da ke jihar Niger zuwa dajin Sambisa da ke Borno.

Shehu ya kara da cewa, babu alamar rahama a fuskokin mutanen.

Jami’in ya ce, fatattakar da dakarun Najeriya ke yi wa ‘yan Boko Haram a arewa maso gabashin kasar ne, ta tilasta wa mutanen yin kaura zuwa Zaria.

Hukumomin Najeriya sun bukaci al’ummar kasar da su sanar da jami’an tsaro da zaran sun ga bakuwar fuskar da ba su yadda da ita ba a unguwanninsu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.