Isa ga babban shafi
Najeriya-Kaduna

An sace wasu 'yan kasar Jamus a jihar Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar da samun rahoton sace wasu yan kasar Jamus guda biyu a kauyen Jajela dake Jihar Kaduna.

Tambarin rundunar 'yan sandan Najeriya
Tambarin rundunar 'yan sandan Najeriya financialwatchngr
Talla

Kakakin ‘yan sandan Aliyu Usman ya ce mutanen kauyen ne suka shaida musu sace mutanen biyu wadanda suka je aiki ba tare da jami’an tsaron dake kare lafiyar su ba.

Ana kyautata zaton cewar masu satar mutane dan karbar diyya ne suka kwashe su.

Jamusawan masu bincike ne na abubuwan tarihi da ke karkashin kasa, wadanda suka ziyarci kauyen Jajela da ke karamar hukumar Kagarko a jihar Kaduna.

A halin da ake ciki, babu wanda ya nemi kudin fansa domin sakin Jamusawan, kamar yadda rundunar yan sanda ta bayyana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.