Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

Dattawan Borno sun bayyana fatansu kan dawowar Buhari

Bayan dawowar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari daga hutun jinya a Ingila, babban abin da dattawa a jihar Borno ke fata shi ne kara inganta sha’anin tsaro a yankin, lura da yadda aka rika samun hare-haren ‘yan kungiyar Boko Haram, a cikin ‘yan makwannin da suka gabata.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Sunday AGHAEZE / NIGERIA STATE HOUSE / AFP
Talla

Yayin zantawarsa da sashin hausa na RFI, Alhaji Muhammadu Mustapha Maikanuri, shugaban al’ummar Kanuri a yankin kudu maso yammacin Najeriya, ya ce bayan dawowar shugaba Buhari, a yanzu suna da yakinin cewa za a samu cigaba ta fannin ingantuwar sha’anin tsaro.

A cewar Maikanuri akwai matukar bukatar gaggauta kawo karshen neman farfadowar da barazanar tsaron ke yi a yankin arewa maso gabashin Najeriya, idan akayi la’akari da yawan tashin bama-bamai ko kuma kai harin kunar bakin wake da aka fuskanta musamman a Borno makwannin da suka gabata.

01:03

Dattawan Borno sun bayyana fatansu kan dawowar Buhari

Abdoulkarim Ibrahim

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.