Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram ta kashe mutane a kasuwar Konduga

Rahotanni daga birnin Maiduguri na jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa, kungiyar Boko Harm ta kaddamar da hare-haren kunar bakin wake a karamar hukumar Konduga, abin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 27.

Boko Haram ta kashe mutane 27 a Konduga da ke jihar Maiduguri
Boko Haram ta kashe mutane 27 a Konduga da ke jihar Maiduguri © AFP PHOTO / BOKO HARAM
Talla

Maharan su tayar da bama-bamai guda biyu a wata kasuwa da ke karamar hukumar kuma a dai dai lokacin da jama’a ke tsaka da cin kasuwancinsu a yammain wannan Litinin kamar yadda wakilinmu, Bilyaminu Yusuf ya tabbatar mana.

Bam na uku ya tashi ne a sansanin ‘yan gudun hijira da ke garin na Kondugan kamar yadda Yusuf ya shaida mana.

Ana fargabar cewa, adadin wadanda suka mutu ka iya karuwa saboda munin farmakin.

Garin Konduga mai tazarar kilomita 30 daga birnin Maiduguri na daya daga cikin yankunan jihar Borno da suka fi fama da hare-haren Boko Haram, lamarin da ke haddasa asarar rayuka da dukiyoyi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.