Wasu mayaka sun kai hari a Adamawa
Wasu mutane da ake zargin ‘yan Boko Haram ne sun kai hare-hare a cikin daren da ya gabata a wasu yankuna na jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Wallafawa ranar:
Mutanen yankunan sun kauracewa gidajensu bayan farmakin da mayakan suka kaddamar a Nyibango da Muduhu da ke karamar hukumar Madagali.
Farmakin na zuwa ne kwanakin kalilan da aka kai makamancinsa a kauyen Mildu da ke makwabtaka da yankunan, in da mutane bakwai suka rasa rayukansu.
A yayin zantawa da manema labarai, shugaban karamar hukumar Madagali, Yusuf Muhammad ya ce, mayakan sun dauki tsawon sa’oi biyu suna kai hare-haren.
Mayakan sun kona gidaje da dama tare da sace kayayyakin abincin jama’a kamar yadda shugaban karamar hukumar ya tabbatar.
A cewarsa, kawo yanzu, ba a tantance adadin mutanen da suka mutu ba da kuma wadanda suka samu rauni.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu