Isa ga babban shafi
Najeriya

Hare-haren kunar bakin wake sun haifar da fargaba a jami'ar Maiduguri

Hare haren kunar bakin wake da aka kai kwanan baya a jami’ar Maiduguri da ke Jihar Borno, ya kara haifar da fargaba da tsoro a tsakanin dalibai da kuma malaman Jami’ar ta fuskar sha’anin tsaro. Kimanin mutane 16 aka tabbatar da sun mutu a hare haren kunar bakin wake guda biyu da aka kai a Jami’ar ta Maiduguri a ranar Lahadi da dare da aka yi bikin Sallah. An sha kai hare hare a Jami’ar amma hakan bai sa an rufe makarantar ba, sai dai a kullum malamai da dalibai na cikin fargaba da daukar matakan kare-kai. Awwal Janyau ya taba kai ziyara Jihar Borno kuma ya diba matsalar tsaron a Jami’ar ta Maiduguri.

Kofar shiga cikin jami'ar Maiduguri
Kofar shiga cikin jami'ar Maiduguri pulse.ng
Talla

03:20

Hare-haren kunar bakin wake sun haifar da fargaba a jami'ar Maiduguri

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.