Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Dr Muntaka Usman: Karuwar marasa aikin yi a Najeriya

Wallafawa ranar:

Hukumar Kididdiga a Najeriya ta ce matsalar rashin ayyukan yi ta karu da sama da kashe 14, a karshen shekarar 2016, inda adadin da ya zarce na 2015. Hakan dai ya nuna adadin ma’aikatan da ke rasa aikin yi na karuwa kamar yadda adadin mararsa ayyukan ke karuwa a Najeriya. Rahoton hukumar na zuwa a yayin da gwamnatin Najeriya ke ikirarin samar da ayyukan yi ga masu zaman banza domin tayar da komadar tattalin arzikin kasar. Awwal Janyau ya tattauna da Dr Muntaka Usman na sashen nazarin tattalin arziki a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria a Najeriya.  

Najeriya na bukatar kirkiro sabbin guraben ayyuka akalla miliyan 4 da dubu 500 duk shekara domin kawo karshen matsalar rashin aikin yi da ke yawaita a tsakanin 'yan kasar.
Najeriya na bukatar kirkiro sabbin guraben ayyuka akalla miliyan 4 da dubu 500 duk shekara domin kawo karshen matsalar rashin aikin yi da ke yawaita a tsakanin 'yan kasar. premiumtimesng
Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.