Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya ta tafka asarar dala miliyan 450

Majalisar dattijan Najeriya, ta bayyana kaduwarta bisa yadda ta ce kasar ta fuskanci hare hare, ko kuma kutsen satar bayanai na shafin Intanet akalla sau 3, 500 a sararin samaniyar dandalin shafukan kasar.

Hoton wasu daga cikin na'urorin komfutar da kusten fasaha mai illa ya shafa a makon da ya gabata.
Hoton wasu daga cikin na'urorin komfutar da kusten fasaha mai illa ya shafa a makon da ya gabata. Reuters
Talla

Yayinda ta ke bayyana kaduwarta majalisar dattijan ta ce sakamakon fuskantar wannan kutse, Najeriya ta yi hasarar dala miliyan 450.

A ranar Talatar nan ce kuma, zauren majalisar ya bukaci mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan tsaro, da ya umarci ilahirin hukumomin tsaron kasar, da su dauki tsauraran matakan kare sararin shafin Intanet na Najeriya.

Sanata Buhari Abdulfatai da ke shugabantar kwamitin majalisar dattijan da ke lura da bunkasa fannin fasahar sadarwa, ya ce tilas a dauki matakan gaggawa, domin kauwacewa fuskantar hadarin sacewa manyan ma’aikatun Najeriya da kamfanoni, muhimman bayanansu kamar yadda aka yi a kasashen duniya 150, makwanni biyu da suka gabata.

Akalla ma’aikatu, manyan asibitoci da kuma kamfanoni sama da 200,000 ne aka yi wa kutse a shafukansu na Intanet, tare da kulle musu muhimman bayanai da suka shafi kididdiga da sauran bayanan sirri.

Daga bisani ne kuma wadanda suka kitsa kai harin suka bukaci da sai an biya akalla dala 300 kan kowace naura mai kwakwalwa da aka kulle muhimman bayanan da jke kanta, kafin sake bude su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.