Isa ga babban shafi
Najeriya

Ba zamu lamunci yunkurin kara farashin mai ba - NUPENG

Kungiyar ma’aiktan mai da hako iskar gas ta Najeriya NUPENG, ta yi ala wadai tare da yin gargadi game da yunkurin kara farashin man fetur, karkashin wani kudiri da aka gabatarwa majalisar dattawan kasar.

Nigeria: The Nigerian Union of Petroleum and Natural Gas Workers (NUPENG) says it is set to oppose any form of proposed N5 petrol levy
Nigeria: The Nigerian Union of Petroleum and Natural Gas Workers (NUPENG) says it is set to oppose any form of proposed N5 petrol levy businessdayonline
Talla

A zantawarsa da kamfanin dillancin labaran najeriya NAN, a Legas, Alhaji Tokunbo Korodo, shugaban kungiyar ta NUPENG reshen kudu maso yammacin Najeriya, ya ce bai kamata a gabatar da kudirin ba, a dai dai lokacin da ‘yan Najeriya ke cikin hali na matsin rayuwa, dan haka kungiyar hadi da dukkanin reshunan na kwadago, ba zasu taba amincewa da wannan yunkuri ba.

Karkashin kudirin, wanda Sanata Kabiru Ibrahim Gaya mai wakiltar Kano ya gabatarwa zauren majalisar dattijan a ranar Juma’ar da ta gabata, za’a rika biyan harajin naira biyar, kan kowace litar, za’a kuma yi amfani da harajin ne, wajen gina manyan hanyoyi a sassan kasar.

Zalika kudirin ya bukaci rage wani adadi na kudaden da fasinjoji ke biya zuwa sassan kasar, a kuma dawo da manyan shin gayen da a baya aka kafa a manyan titunan gwamnatin tarayya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.