Isa ga babban shafi
Najeriya

Attajirai kawai ke amfana da habakar tattalin arziki a Najeriya

Kungiyar Agaji ta OXFAM ta bayyana cewar attajiran Najeriya guda biyar da suka mallaki dukiyar da ta kai Dala biliyan kusan 30 na iya magance tsananin talaucin da ya addabi al’ummar kasar.

Attajiran Najeriya guda biyar na iya magance tsananin talaucin da ya addabi al’ummar kasar
Attajiran Najeriya guda biyar na iya magance tsananin talaucin da ya addabi al’ummar kasar MUSBIZUBET.COM
Talla

Rahotan da kungiyar ta OXFAM ta fitar mai taken banbanci a Najeriya, ya yi nazari ne kan gibin da ke tsakanin attajirai da matalauta, inda ya ke cewar attajiran Najeriyar ne kawai suka amfana da habakar tattalin arzikin da aka samu, yayin da talakawa ke ci gaba da rayuwa cikin kunci.

Kungiyar OXFAM ta ce 'yan Nageriya sama da miliyan 112 ke zama cikin kuncin talauci, yayin da mutumin da yafi kowa kudi a kasar ke iya kasha Dala miliyan guda kowacce rana har na shekaru 42.

Rahotan ya kuma ce 'Yan Najeriya kashi 69 ke rayuwa kasa da mizanin duniya a Yankin Arewa Maso Gbaashin Kasar, yayin da adadin ya ragu a kudu maso yammacin kasar zuwa kashi 49.

OXFAM ta kuma ce tsakanin shekarar 1960 zuwa shekarar 2005 masu rike da ofisoshin gwamnati sun sace dukiyar da ta kai Dala Triliyan 20, yayin da jami’an gwamnati suka yafewa manyan kamfanonin kusan Dala biliyan 3 wajen biyan haraji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.