Biafra: Yadda al'amura suka kasance a kudancin Najeriya
Kasuwanni da makarantu sun kasance a rufe a yankin kabilar igbo, da ke kudu maso gabashin Najeriya bayan kungiyoyin da ke fafutukar kafa kasar Biafra suka yi kira ga jama’ar yankin da su kasance a gida, yayinda ake cika shekaru 50 da Chukwuemeka Ojukwu ya kaddamar da yakin neman tabbatar da kasar Biafra.
Wallafawa ranar:
Kasuwanni dai sun kasance a rufe a biranen Enugu da Owerri da kuma Aba, yayinda kuma bankuna suka kasance a rufe, illa wasu ma’aikatan da ke gudanar da ayyukansu a cikin ofisoshi.
Muhammad Lawal dan Tibi mazauni a garin Enugu, kuma mai magana da yawun ‘yan arewa mazauna yankin na kudu maso gabashin Najeirya, yayinda zantawarsa da RFI Hausa, ya ce ba’a samu tashin hankali a garin ba.
Sai ma wasu daga cikin shugabannin Coci da suka yi wa shugaban Najeriya addu’ar samun lafiya, da kuma bayyana cigaba da neman kafa kasar Biafra a matsayin koma baya ga yankin.
Biafra: Yadda al'amura suka kasance a kudancin Najeriya
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu