Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya: Za'a dakatar da jami'an gwamnati da aka zarga da almundahana

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bai wa kwamitin da ke bincika zargin aikata almundahana da ake wa sakataren gwamnati da aka dakatar, Babachir Lawal da babban daraktan hukumar NIA Ayo Oke, umarnin dakatar da dukkanin jami’an gwamnatin da ke da alaka da laifukan da manyan jami'an biyu suka tafka.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. REUTERS
Talla

Shugaba Buhari dai ya bukaci kwamitin ya dakatar da wadanda ake zargin ne kafin kammala aikinsa na makwanni biyu.

Kwamitin mai kunshe da mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin shugaba, ministan shara’a Abubakar Malami, da kuma mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaro Babagana Mungonu, yana bincike ne kan zargin da ake wa sakataren gwamnati Babachir Lawal bisa bawa kamfanin kwangilar sama da naira miliyan 200 don share ciyawa a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Zalika kwamitin wanda ya fara aikinsa a ranar Larabar da ta gabata, yana gudanar da bincike kan, dala miliyan 43 da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC ta gano a wani gida, da ke unguwar Ikoyi a jihar Legas, wanda kuma ake zargin darakatan hukumar tattara bayanan sirri ta kasar NIA Ayo Oke da masaniya kan kudin, bayanda yayi ikirarin cewa kudaden mallakar hukumarsa ce.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.