Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya dakatar da Babachir da shugaban NIA

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dakatar da Sakataren Gwamnatin Tarayya David Lawal Babachir da shugaban Hukumar leken asiri ta kasa NIA Ayodele Oke kan zarge-zargen rashawa da ake wa jami’an.

Sakataren Gwamnati David Lawal Babachir
Sakataren Gwamnati David Lawal Babachir http://newsverge.com
Talla

Buhari ya kuma kafa kwamitin mutane 3 a karkashin mataimakinsa Yemi Osibanjo domin binciken mutanen biyu cikin mako biyu tare da gabatar da ma sa da rahoto.

Ana tuhumar Babacir Lawal ne da bada kwangila ta hanyar da ba ta kamata ba, yayin da ake tuhumar Oke da makudan kudaden da aka samu a wani gida da ke Lagos da yawan su ya kai naira biliyan 13.

Shugaba Buhari ya dakatar da Babachir har sai an kammala bincike.

Sauran ‘Yan kwamitin binciken sun hada da ministan shari'a Abubakar Malami da Mai ba Buhari shawara kan harkokin tsaro Janar Mohammed Mongono.

Masu sa ido a yaki da cin hanci da rashawa da dama sun dade suna kokawa kan rashin daukar mataki kan manyan jami'an gwamnatin Buharin da ake zargi da aikata laifukan rashawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.