Isa ga babban shafi
Najeriya

Ya kamata EFCC ta gaggauta sanar da masu kudin Ikoyi- Saraki

Majalisar Dattawan Najeriya ta bukaci hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar EFCC, da ta gaggauta bayyana mamallakan makuden kudaden da yawansu ya kai Dala Miliyan 43, wanda aka gano a wani kasaitaccen gida da ke unguwar Ikoyi a jihar Legas. 

Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya Bukola Saraki
Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya Bukola Saraki REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

A wata zantawa da ya yi da manema labarai, shugaban Majaliar Dattawan Bukola Saraki ya ce, cecekucen da ake ci gaba da yi kan kudaden na dakushe martabar Najeriya.

Mr. Saraki ya ce, EFCC ce ke da alhakin kawo karshen cecekucen da ake yi ta hanyar bayyana ainihin mutanen da suka tara makudaden kudaden a cikin gidan na Ikoyi.

Rohatanni sun ce, ko a jiya Talata, sai dai hukumar ta EFCC ta sake samame a gidan, in da a wannan karo ta binciki sassan tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi da kuma tsohon shugaban jam’iyyar PDP mai adawa, Alhaji Ahmad Adamu Mu’azu.

Wannan na zuwa ne bayan wasu jami’an leken asiri sun ce, akwai yiwuwar an boye wasu kudaden daban a sassan gidan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.