Isa ga babban shafi
Najeriya

Abdul'aziz Yari ya mayarwa Sarki Sunusi martani

Ga alama kalaman Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu, kan matsayin Gwamnan Jihar Zamafara dangane da dalilin samun cutar sankarau bai yiwa Gwamna Abdulaziz Yari dadi ba, ganin yadda ya nuna fushin sa kan matsayin Sarki.

Gwamnan Jihar Zamfara Abdul'aziz Yari
Gwamnan Jihar Zamfara Abdul'aziz Yari RFI
Talla

Sarkin dai ya bayyana cewar bai da ce a danganta barkewar cutar da ayyukan da mutane ke yi ba, inda ya bukaci nemo maganin cutar dan yiwa jama’a rigakafi.

Yayin da ya ke mayar da martani ga Sarkin, Gwamnan ya ce ya yi amfani da nafsi da hadisi ne wajen bayyana matsayin sa.

Kuma a matsayin sa na gwamna Zamfara ya dauki duk matakan da suka da ce wajen ganin an tallafawa mutanen da suka kamu da cutar a Jihar sa.

Ku saurare raddi Yari kan kalaman Sarki Sunusi.

01:04

Gwamnan Zamfara Abdul'aziz Yari

Umaymah Sani Abdulmumin

Abdul'aziz Yari dai ya ce yana nan aka bakansa kuma babu abin da zai sauya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.