Isa ga babban shafi
Najeriya

Sarkin kano ya soki kalaman Gwamna kan sankarau

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ya ce kuskure ne kalaman Gwamnan Zamfara Abdul'aziz Yari cewar laifufukan jama'a ne suka haifar da annobar cutar sankarau da ta hallaka mutane sama da 200 a Jihar yanzu haka.

Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na II
Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na II
Talla

Sarkin da ke jawabi wajen wani taron zuba jari a Kaduna ya ce wannan matsayi na gwamnan ya sabawa shari'ar Islama.

Basaraken ya ce idan Zamfara ba ta da maganin rigakafi, nema ya kamata ta tafi a inda ake samar da shi, maimakon danganta annobar da aikata laifuffuka.

Kalaman Gwamnan Jihar ta Zamfara Abdulaziz Yari ya janyo masa suka daga sassa daban daban ganin cewar Jihar ita ce tafi fuskantar annobar wanda yanzu haka aka bayyana cewar mutane 214 suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.