Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya na bukatar Dala biliyan 1.1 don yaki da Sankarau

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ana bukatar Dala biliyan 1 da miliyan 100 don yaki da annubar sankarau a jihohi biyar da ke yankin arewa maso gabashin kasar.

Najeriya na bukatar Dala biliyan 1 da miliyan 100 don yaki da annubar Sankarau a jihohi biyar na arewacin kasar
Najeriya na bukatar Dala biliyan 1 da miliyan 100 don yaki da annubar Sankarau a jihohi biyar na arewacin kasar
Talla

Wannan na zuwa ne bayan shugaban Majalisar Dattawan kasar Sanata Bukola Saraki ya bayyana cewa, a shirye suke su bai wa gwamnati hadin kai don magance annubar.

Mukaddashin shugaban Hukumar Bunkasa Ayyukan Lafiya a matakin farko ta kasar Dr. Emmanuel Odu ya bayyana cewa, za a yi amfani da kudaden don samar da rigakafin cutar ga mutane miliyan 22 a jihohin Zamfara da Sokkoto da Kebbi da Katsina da Niger, in da jumullar mutane 328 suka rasa rayukansu.

Kawo yanzu dai annubar ta yadu zuwa jihohi 16 na Najeriya, in da aka samu rahoton da ke cewa, kimanin mutane dubu 2 da 524 sun kamu da ita.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.