Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya za ta yi aiki da karnuka don dakile harin bam

Babban Hafsan sojin kasa ta Najeriya laftanar janar Tukur Buratai ya bada umurni kawo kwararun karnuka masu basira don aikin gano bama-bamai a jikin ‘yan kunar bakin wake, in da za a tura su lunguna da sako na bayan gari.

Najeriya za ta fara aiki da karnuka  don yaki da masu da tayar da bam a jihar Borno
Najeriya za ta fara aiki da karnuka don yaki da masu da tayar da bam a jihar Borno ©Reuters.
Talla

Wannan na zuwa ne bayan wani kare ya hana wata ‘yar kunar bakin wake kutsawa cikin taron biki a kauyen Balbelu da ke jihar Borno don tada bama-baman da ta yi damara da su.

Mamallakin karen Alhaji Malu ya shaida wa RFI Hausa cewa, karen nasa da ‘yar kunar bakin waken duk sun mutu bayan ya uzura ma ta, in da ya hana ta shiga cikin jama’a don kashe su.

Alhaji Malu ya ce ya damu matuka da mutuwar karensa lura da shakuwar da ke tsakaninsu.

Wakilinmu Bilyaminu Yusuf ya je wannan kauyen kuma ga rahoton daya aiko mana.

01:30

Rahoto kan amfani da karnuka a yaki da 'yan kunar bakin wake

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.