Najeriya na bukatar taimako don share nakiyoyin da Boko Haram ta dasa
Babban Hafsan sojin Najeriya Laftanat Janar Tukur Buratai, ya bukaci taimakon kwarraru daga Majalisar Dinkin Duniya, wajen share nakiyoyin da mayakan Boko Haram suka dasa a yankunan da suka taba kwacewa, musamman dajin Sambisa.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Buratai ya bukaci taimakon ne yayin zantawa da manema labarai a garin Maiduguri, inda ya ce yawan nakiyoyin da mayakan suka binne yana kange sojoji isa zuwa wasu sassan dajin na Sambisa.
Masana harkokin tsaro dai sun ce da bukatar a gudanar da wannan aikin cikin gaggawa ganin hadurran dake tattare da barinsu na tsawon lokaci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu