Isa ga babban shafi
Najeriya

Kwamandan mayakan Boko Haram ya mika kansa

Rundunar sojin Najeriya, ta ce daya daga cikin manyan kwamandojin kungiyar Boko Haram, Bulama Kailani Muhd Metele, ya mika kansa ga bataliyar rundunar ta 145, da ke garin Damasak a jihar Borno.

Daya daga cikin hoton bidiyon da mayakan Boko Haram ke watsawa a shafin Internet.
Daya daga cikin hoton bidiyon da mayakan Boko Haram ke watsawa a shafin Internet. AFP PHOTO / BOKO HARAM
Talla

Yayin tabbatar da hakan yau a garin Maiduguri, kakakin sojin Najeriya, Birgediya Janar Sani Usman, ya ce Metele, ya fito ne daga bangaren shugabancin kungiyar Boko Haram karkashin Mamman Nur.

Bulama Metele, shi ne mutum na 253, cikin mayakan Boko Haram, da rundunar sojin Najeriya ta yi shelar nemansu ruwa a jallo.

Birgediya Janar Usman ya ce sojin bataliya ta 158 sun kuma kama wasu ‘yan leken asirin kungiyar ta Boko Haram, a kauyukan Kareto da Dangali, kuma bicikensu ya nuna cewa, suna leken asirin ne saboda shirin kai harin ta'addanci kan kauyukan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.