Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya yi alkawarin yin sulhu da tsagerun Niger Delta cikin 2017

Shugaban Najeriya Muhd Buhari, ya sha alwashin yin sulhu da tsagerun yankin Niger Delta cikin sabuwar shekara da muka shiga, don kawo karshen fashe fashen bututun mai a yankin.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Talla

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne, cikin sakon taya murnar al’ummar kasar shiga shekara ta 2017.

Fasa butun mai babu kakkautawa da tsagerun yankin na Niger delta suka rika yi, ya taimaka wajen nakasa tattallin arzikin Najeriya da danyen man fetur ke taka muhimmiyar rawa a cikinsa.

To sai dai kuma kama daga watan Nuwamban da ya gabata, an samu raguwar fasa bututun man da tsagerun ke yi, bayan tattaunawar da ta gudana, tsakanin shugaba Buhari da wakilan yankin.

A baya dai Najeriya na hako gangar danyen mai akalla miliyan biyu da dubu dari a kowace rana, amma sakamakon hare haren tsagerun yankin Niger Delta ya tilasta rage yawan gangar da ake haka kowace rana da kasha daya bisa uku.

Sai dai kuma a halin yanzu Minstan albarkatun man kasar Dr Ibe Kachikwu ya ce sakamakon gyara da dama daga cikin jerin bututunm man da aka fasa, yawan gangar danyen man da Najeriya ke fitarwa a kowace rana ya karu zuwa miliyan daya da dubu dari takwas.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.