Isa ga babban shafi
Najeriya

MEND ta nesanta kanta da taron sulhu

Kungiyar MEND dake ikrarin yantar da Yankin Naija Delta ta nesanta kanta da wani taro da Edward Clark da Gwamnan Jihar Delta suka gudanar dan samo maslaha kan halin da Yankin ya samu kan sa.

'Yan Kungiyar MEND dake faffutukar yantar da yankin Niger Delta a Najeriya
'Yan Kungiyar MEND dake faffutukar yantar da yankin Niger Delta a Najeriya AFP/PIUS UTOMI EKPEI
Talla

Sanarwar da mai Magana da yawun kungiyar Jomo Gbomo ya rabawa manema labarai, ya bukaci gwamnatin Najeriya tayi watsi da sanarwar bayan taron da akayi, inda kungiyar ke cewa Edward Clark bashi da halarcin jagorancin duk wata tattaunawa da gwamnati, domin lokacin tsohuwar gwamnatin da ta gabata, da shi aka tafka kura kurai.

Sanarwar ta kuma bayyana yadda taron yaki Allah wadai da ta’asar da kungiyar Naija Delta Avengers keyi, inda ta bayyana goyan bayan ta ga shirin sasantawa da gwamnatin Najeriya.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar 'Yan bindigan Niger Delta Avengers ke cewa sun shirya ganawa da wakilan gwamnatin kasar don dakatar da hare-haren da suke kaiwa akan bututan mai dake matukar yiwa tattalin arzikin kasar ta'annati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.