Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya bukaci a kwantar da hankalin 'yan Niger Delta

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci shugabanin al’ummomin Niger Delta da su kwantar da hankalin mabiyansu wadanda ke tada kayar baya kan halin da yankin ya samu kansa, inda yake cewa a shirya yake ya inganta rayuwarsu tare da na sauran 'yan Najeriya.

Shugaban Najeriya  Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari AFP PHOTO / STRINGER
Talla

Shugaban ya bayayan damuwarsa kan yadda ake ci gaba da samun tashe-tashen hankalu a yankin da kuma kai hare-hare kan bututun mai, matakin da ya haifar da koma baya dangane da yawan man da Najeriya ke fitar wa wanda ya shafi tattalin arzikin kasar da kuma jefa ta cikin rashin wadatacciyar wutar lantarki.

Shugaba Buhari ya ce, suna son sake gina Najeriya baki daya bayan an yi mata lahani sosai kamar yadda ya shaida wa wakilan al'ummomi a ganawar da ya yi da su a fadarsa da ke Abuja a jiya Alhamis

Tsagerun Niger Delta dai na bukatar gwamnatin kasar da ta rika ware musu wani kaso mai tsoka daga cikin kudaden da ta ke samu na man fetir.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.