Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya ta kulla yarjejeniya da Avengers

Gwamnatin Najeriya ta sanar da kulla yarjejeniyar tsagaita wuta har tsawon wata guda tsakaninta da kungiyar tsagerun Niger Delta da ke kai hare hare, inda suke fasa bututun man fetir.

Gwamnatin Najeriya ta kulla yarjejeniyar tsagaita musayar wuta ta wata guda da tsagerun Niger Delta
Gwamnatin Najeriya ta kulla yarjejeniyar tsagaita musayar wuta ta wata guda da tsagerun Niger Delta AFP/PIUS UTOMI EKPEI
Talla

Gwamnatin ta bayyana cewar daga cikin kungiyoyin da suka amince da shirin tsagaita wutar har da kungiyar Niger Delta Avengers wadda ke kai hare hare ba kaukautawa a ‘yan kwanakin nan.

Sakataren kungiyar kasashe masu arzikin man fetir, Muhammad Barkindo ya tababtar wa RFI hausa da wannan labarin bayan ya gana da shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja da kuma ministan mai Ibe Kachikwu.

Barkindo ya ce, adadin man da Najeriya ke samarwa ya fara karuwa, abinda zai taka rawar gani dangane da kudin shiga da kasar ke samu.

00:54

Muhammad Barkindo kan Niger Delta Avengers

A makon jiya ne, kungiyar tsagerun Niger Delta ta gindaya sharuddan tattaunawa da gwamantin, inda ta ce, ba ta amince masu shiga tsakani daga kasashen ketare su tsoma baki cikin lamarin ba.

Tsagerun dai na bukatar gwamnatin Najeriya da ta rika ware wani babban kaso na kudin da ta ke samu daga man fetir domin bai wa yankin na Niger Delta.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.