Isa ga babban shafi
Najeriya

Gwamnatin Najeriya za ta yi sulhu da Avengers

Najeriya ta sanar da shirinta na gudanar da tattaunawar Sulhu da tsagerun Neja Delta masu kai hare-hare kan bututu da rijiyoyin mai dake kudancin kasar.

AFP Photo/Pius Utomi Ekpei
Talla

Rundunar Sojin kasar ta aika da jiragen yaki dana ruwa yankin domin murkushe tsagerun dake ci gaba da tana’anti ga tattalin arzikin kasar, sai dai karamin Ministan Mai Dr Ibe Kachikwu yace zasu baiwa tsagerun mako daya zuwa biyu don gani ko za a cimma daidaito.

A makon da ya gabata ma dai wasu Manyan kamfanonin mai guda biyu a Najeriya sun sanar da cewar suna tafka asarar ganga 140,000 kowacce rana sakamakon kazamin harin da kungiyar mayakan Niger Delta Avengers ke kaiwa kayan aikin su

Karamin Ministan man Najeriya Ibe Kachikwu yace Najeriya na samar da gangar mai miliyan daya da dubu dari shida kowacce rana sabanin ganga miliyan biyu da dubu dari biyu da aka saba sakamakon illar da Avengers ke yiwa harkar mai.
 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.