Wata sabuwar kungiyar Niger Delta ta yi barazanar kai hare hare
Wata sabuwar kungiyar matasa da ke dauke da makamai a yankin Niger Delta mai arzikin mai a Najeriya da ke kiran kanta Joint Niger Delta Liberation Force, ta ce za ta kaddamar da hare-hare domin lalata kadarorin gwamnati da aka gina da kudin mai na kasar, wanda kungiyar ta bayyana shi a matsayin arziki mallakin ‘yan yankin.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Daga cikin wuraren da kungiyar ke shirin kai wa hari sun hada da fadar shugaban kasa da majalisun dokoki da ma’aikatun gwamnati da ginin kamfanin mai na NNPC, da babban bankin kasar da kuma barikokin soji.
Cikin sanarwar da kungiyar ta rabawa manema labarai tace za ta jefa gwamnati cikin kunci kamar yadda mutanen Niger Delta ke cikin kuncin rayuwa sakamakon gurbata muhallin yankin.
Wannan barazanar na zuwa ne bayan gwamnatin Muhammadu Buhari ta kaddamar da aikin tsabtace yankin Ogoni da tsiyayar mai ya lalata wa mutanen yankin muhallinsu.
Barnar da tsagerun Niger Delta suka aikata a bututun mai ya janyo wa Najeriya hasara, inda kasar ta koma fitar da danyen mai ganga 1.4 a rana maimakon ganga miliyan 2.2 a rana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu