Isa ga babban shafi
Najeriya

An sake gano dalibar Chibok a Damboa

Rundunar sojin Najeriya ta sanar da sake ceto wata ‘yar sakandaren garin Chibok daga hannu mayakan Boko Haram, sanarwar dake zuwa bayan shugaba buhari ya gana da Amina Ali Nkike yarinya ta farko da aka kubutar daga hannu mayakan a ranar talata.

'Yan matan sakandaren garin Chibok da Mayakan Boko Haram ke garkuwa da su a Najeriya
'Yan matan sakandaren garin Chibok da Mayakan Boko Haram ke garkuwa da su a Najeriya via CNN
Talla

Kakakkin rundunar Sojin Najeriyar Kanar Sani Usman ya ce dakarunsu da taimakon ‘yan kato da goro sun sake gano yarinya ta biyu Serah Luka da misalin 11 safe a yankin Damboa dake Bornon arewacin Najeriya.

A cewar Kanar Sani, Serah ‘yar gidan wani Faston Mujimi’a ne ‘yan asalin Madagali dake jihar Adamawa.

01:32

Kanar Sani Usman kan Ceto 'yar Chibok ta biyu

Umaymah Sani Abdulmumin

A jiya ne Daliba ta farko Amina Ali da mahaifiyarta suka gana da shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari a fadarsa dake Abuja, inda shugaban ya yi alkawarin cewa gwamnati za ta dau dawainiyarta.

Ceto Amina shi ya sake karawa gwamnatin Najeriya kwarin Gwiwa a kokarin da suke wajen ceto daliban sakandaren garin Chibok sama da 200 da mayakan Boko Haram sukayi garkuwa da su shekaru biyu da suka gabata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.