Isa ga babban shafi
Najeriya

An gano wata ‘Yar Chibok a Dajin Sambisa

Amina Ali na daga cikin ‘Yan Matan Chibok 219 da aka sace kuma a jiya Talata ne ‘Yan kato da gora da ke taimakawa Sojin Najeriya suka kubutar da ita daga Dajin Sambisa tare da gabatar da ita ga iyayenta a garin Mbalala kusa da Chibok.

Hoton Amina Ali tare da yarta Safiya da ta haifa da wani dan Boko Haram
Hoton Amina Ali tare da yarta Safiya da ta haifa da wani dan Boko Haram REUTERS
Talla

A cikin wata sanarwa, Kanal Usman Kukasheka ya tabbatar da kubutar da dalibar ta makarantar Chibok.

An gabatar da Amina mai shekaru 17 ga iyayenta kafin daga bisani aka tafi ta da ita zuwa sansanin Soji a Damboa.

A ranar 14 ga watan Afrlu ne ‘Yan Boko Haram suka abka Makarantar sakandaren garin Chibok suka yi awon gaba da dalibai mata 276. Amma daga baya wasu 57 daga cikin ‘Yan matan sun tsere daga hannun mayakan.

Zuwa yanzu gwamnatin Najeriya ba ta ce komi ba game da kubutar da Amina.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.