Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya gana da 'yar Chibok

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da daya daga cikin ‘yan matan sakandaren garin Chibok da aka ceto daga hannu mayakan Boko Haram Amina Ali Nkike.

'Yar Chibok Amina Ali Nkike a Fadar Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari
'Yar Chibok Amina Ali Nkike a Fadar Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari
Talla

Amina da aka ceto da taimakon ‘yan kato da gora a ranar talatar data gabata, ta isa fadar shugaban kasa da mahaifiyarta Binta da kuma gwamnan jihar Borno Kashim Shettima da wasu jami’an gwamnati da suka hada da babban hafsan tsaron kasar.

Gano Amina yanzu ya sake baiwa gwamnati kasar kwarin gwiwa a kokarin da ake wajen ceto ‘yan mata da akayi awan gaba dasu sama da shekaru biyu.

Yarinyar da akayi garkuwa da ita lokacin tana mai shekaru 17, ta shaida cewa 6 daga cikin ‘yan mata dake hannu mayakan sun rasa rayukansu, yayin da sauran ke dajin Sambisa.

Shugaban Buhari a ganawarsa da Amina, ya yi alkawarin cewa gwamnati zata bata cikakkiyar kulawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.