Isa ga babban shafi
Najeriya

Majalisar Najeriya ta gayyaci mai tuhumar Saraki

Kwamitin majalisar dattawa da ke kula da da’a da koken jama’a ya gayyaci mai shari'a Danladi Umar, shugaban kotun ladabtar da ma’aikatan Najeriya da ke shariar Bukola Saraki.

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Bukola Saraki.
Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Bukola Saraki. ynaija.com
Talla

Rahotanni sun ce, kwamitin ya bukaci mai Mr. Umar da ya bayyana a gabansa a ranar Alhamis mai zuwa da misalin karfe 2 na rana agogon kasar.

Kwamitin ya ce, ya yi wannan gayyatar ce saboda zarge zargen da ake yi wa  mai shari'a Umar.

Sai dai hakan na zuwa ne bayan kotun ladabtar da ma'aikatan ta ce, za ta ci gaba da tuhumar Saraki a kullum daga misalin karfe 9 na safe zuwa 6 na yamma, amma za a rika tafiya hutun sa’a guda.

Mr, Saraki wanda shi ne shugaban majalisar dattawan Najeriya na fuskantar tuhuma ne akan laifuka daban daban har guda 13 da ke da nasaba da yin karya game da kadarorin da ya mallaka.

Saraki dai ya rasa samun nasara a kokarinsa na ganin an dakatar da kotun daga yi ma sa tuhuma yayin da a ranar jumma’ar da ta gabata, kotun tarayya da ke birnin Abuja ta yi watsi da bukatarsa ta dakatar da tuhumar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.