Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya kammala hutun kwanaki biyar

A yau Alhamis shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya koma bakin aiki bayan ya dawo daga tafiyarsa ta hutun kwanaki biyar da ya dauka.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari statehouse
Talla

Jirgin shugaban wanda ya taso daga Ingila, ya isa filin jiragen sama na Nnamdi Azikwe da ke babban birnin Abuja da misalin karfe takwas da minti arba’in da biyar na dare agogon kasar a jiya laraba.

A makon jiya ne, bayan ya halarci taron sasanta rikicin Syria a birnin Landan, shugaba Buhari ya sanar da tafiyarsa hutu, lamarin da ya sa ya mikia ragamar  tafiyar da shugabancin kasar a hannun mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbanjo.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.