Buhari ya gargadi Turai kan Libya
Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci kasashen duniya dasu taimaka wajen kawo karshen rikicin kasar Libya, inda yayi gargadi cewa yana iya shafar sauran kasashen Africa dama Turai.
Wallafawa ranar:
Muhammadu Buhari dake magana a Strausbourg na kasar Faransa a jawabinsa daya gabatar gaban wakilan majalisar kasashen Turai yace yadda abubuwa ke tafiya musamman a kudancin Libya na da ban tsoro domin hatta Najeriya ba ta tsira ba, kasancewa makamai dake shiga Najeriyan daga kasar Libya ake kaisu.
Kungiyar Kasashen Turai da Majalisar Dinkin Duniya na goyon bayan ganin a kafa Gwamnatin hadaka ne akasar Libya.
Tun a shekarar 2014 kasar Libya ke karkashin Jagoranci Gwamnatoci biyu da ‘yan majalissar dokoki, inda amintacciyar gwamnatin kasar ga kasashen duniya ke da shedikwata a gashin birnin Tobruk, yayin da daya bangaren gwamnati ta ‘yan tawaye ke zamanta a Tripoli.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu