Isa ga babban shafi
Najeriya

Za mu sa ido ga alkawullan Buhari- PDP

Jam’iyyar PDP mai adawa a Tarayyar Najeriya, ta ce za ta zura ido domin ganin yadda gwamnatin Muhammadu Buhari za ta aiwatar da kasafin kudin kasar na badi, wanda shugaban ya gabatarwa ‘yan majalisar kasar a ranar talata.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudi sama da na Naira Tiriliyon 6
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudi sama da na Naira Tiriliyon 6 REUTERS
Talla

Mataimakin sakataren yada labaran PDP Abdullahi Jalo ya ce batun kirkiro da gurabobin ayyukan yi da shugaba Buhari ya yi alkawari, ba wani bakon abu ba ne domin  Jam'iyyarsu ce ta soma yin haka.

Shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudin na Naira Tiriliyon 6.08, wanda ya kunshi kashi 20 na kudaden da gwamnatin za ta kashe.

An ware kudi Naira Biliyan 433.4 ga ayyukan hanyoyi da Wuta da gidaje. Sannan kudi Naira biliyan 202 aka ware wa bangaren Sufuri.

Shugaba Buhari yace kasafin kudin zai taimaka wajen farfado da tattalin arzikin Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.