Isa ga babban shafi
Najeriya

EFCC ta kame wasu kusoshin gwamnatin Jonathan

Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa a Najeriya ta kama wasu tsoffin manyan jami’an gwamnatin kasar saboda zargin da hannu a cikin badakalar sayen makamai.

Ambasada Bashir Yuguda, tsohon karamin Ministan Kudi a Najeriya
Ambasada Bashir Yuguda, tsohon karamin Ministan Kudi a Najeriya thenation
Talla

Rahotanni sun ce cikin wadanda aka kama har da tsohon ministan kudi Alhaji Bashir Yuguda da wasu jami’an ofishin tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro wadanda yanzu haka suna can suna yi wa hukumar bayanai akai.

Kwamitin binciken da gwamnatin kasar ta kafa ya bayyana cewar an karkata akalar makudan kudade daga cikin naira biliyan 643 da ya kamata a sayi makamai da su, matakin da ya jefa jami’an tsaron kasar da kuma fararen hula cikin hatsari a yakin da Najeriya ke yi da mayakan Boko Haram.

A jiya Litinin ne Jami’an EFCC suka kame Bashir Yuguda da Halliru Bello tsohon Ministan tsaro da kuma dan tsohon gwamnan Sakkwato Attahiru Bafarawa.

Tun tuni ne dai Sambo Dasuki tsohon mai ba Goodluck Jonathan shawara kan sha’anin tsaro ke fuskantar shari’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.