Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya nada kansa a matsayin Ministan Mai

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada kansa a matsayin Ministan Man Fetur na kasar yayin da ake sa ran cewa a yau laraba zai gabatar wa Majalisar kasar sunayen Ministocinsa domin tantance su da kuma amincewa kamar yadda ya yi alkwari.

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari. Francois Picard/France 24
Talla

A lokacin da ya ke zantawa da ‘Yan Jaridu a ranar Talata a birnin New York na Kasar Amurka bayan ya kammala jawabin a gaban shugabannin kasashen duniya, Buhari ya jaddada cewa shine zai rike mukamin Ministan Mai na Najeriya, amma ya ce, zai nada karamin Minsiatan Mai.

A cewar Shugaba Buhari, ya dauki wannan matakin ne a wani yunkuri na tsaftace ma’aikatar Man Fetur ta Najeriya daga matsalar cin hanci da rashawa da ya hada da sace sacen danyan Mai.

Buhari dai ya kwashe tsawon watanni 4 kan karagar mulki ba tare da Ministoci ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.