Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan Majalissar dattawa 83 sun yi amana da Shugabancin Saraki

‘Yan majalisar dattawan Najeriya a yau talata sun jefa kuri’ar tabbatar da amana ga Shugaban majalisar Bukola Saraki, a dai-dai lokacin kotu ke zargin sa da rashawa.Batun da ya haifar da rudu a zauran Majalisar.

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Bukola Saraki Lokacin ranstsuwar kama aiki
Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Bukola Saraki Lokacin ranstsuwar kama aiki REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

‘Yan majalisa 83 ne suka amince da shugabancin Saraki, a dai-dai lokacin da ake cewa akwai baraka tsakanin ‘yan majalisar da suka fito daga jam’iyyar APC mai mulki.

Sanatoci dai a zamansu bayan hutun makonni sun nuna goyon bayansu ga Saraki wanda a yanzu haka ke fuskantar tuhumar yin karya wajen bayyana kaddarorinsa a lokacin da yake gwamnan Kwara.

Duk da dai Saraki ya musanta zarge-zargen da ake yi bayan ya bayyana a gaban kotun kula da da'ar ma'aikata a makon da ya gabata.

Tun lokacin da aka zabi Saraki a matsayin shugaban majalisar dattawan kasar ake samun takun saka tsakanin sa da wasu shugabannin jam'iyyarsa ta APC.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.