Isa ga babban shafi
Najeriya

Bukola Saraki ya sha jifa a Masallacin Idi

Hatsaniya ta barke a Masallacin Idi Jihar Kwara da ke arewacin Najeriya bayan wasu mutane sun yi amfani da ledojin ruwa da duwatsu wajen yi jifa a kan tawagar manyan Jami’an Gwamnati da suka je Sallar Idi, cikin su kuwa har da Shugaban Majalisar dattijai na kasar Sanata Abubakar Bukola Saraki.

Bukola Saraki Yayin karban Rantsuwar kama aiki
Bukola Saraki Yayin karban Rantsuwar kama aiki REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Hatsaniyar da ta barke a filin Idi birnin Jihar na Ilori wasu Shaidu gani da ido sun ce mutanen da suka yi jifan Ma’aikatan Gwamnati ne da ke fushi kin rashin biyan su albashi domin Siyan ragon laya bikin Sallah.

Rahotanni sun ce an Jiyo mutanen sun ta ihun cewar,  a biya su albashinsu.

Toh sai dai daga bisani jami'an tsaro sun yi kokarin kubutar da Bukola Saraki da gwamnan jihar, Abdulfatah Ahmed da kuma sauran kusoshin gwamnati.

Yayyin da wasu majiyoyi ke cewa wadanda suka tayar da hatsaniyar sun yi barna kan ababan hawa Gwamnati.

Daga cikin wadanda aka yiwa jifa akwai Sarkin Ilorin Ibarahim Sulu Gambari da Shugaban Limamin masallacin Idi Ilorin da kuma tsohon Ministan wasanni da dai sauransu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.