Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya mika sunayen Ministoci

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Sanata Bukola Saraki ya tabbatar da cewa Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya aike masa da sunayen mutane da yake son su zama Ministoci.

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari AFP via telegraph
Talla

Sanata Saraki wanda ya tabbatar da samun sunayen a shafinsa na Twitter bai dai bayyana wadanda ke cikin jerin sunayen ba.

Babban ma'aikaci a fadar shugaban kasa, Alhaji Abba Kyari ne da mataimakin shugaban kasa a kan harkokin majalisar dattijai, Sanata Ita Enang ne,suka mikawa Saraki takardar Sunayen.

Shugaba Buhari dai daman ya yi alkawarin bayyana sunayen Ministocin a karshan wannan wata, kuma tuni ya sanar da kansa a matsayin wanda zai kula da ma'aikatar harkokin man feturin kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.