Isa ga babban shafi
Nijeriya

Barakar da aka samu a jami'yar PDP mai mulki a Najeriya

A Nigeria rikicin jam’iyar PDP mai mulkin kasar na ciggaba da dauke hankali, ganin yadda wasu yan Majalisar wakilan kasar daga Jam’iyar 57, suka futo karara tareda bayyana goyan bayan su ga sabuwar Jam’iyar a karkashin Abubakar Kawu Baraje.

Wasu daga cikin kusoshin jam'iyar mai mulkin a  Nijeriya
Wasu daga cikin kusoshin jam'iyar mai mulkin a Nijeriya
Talla

A sanarwar da suka rabawa manema labarai dauke da sanya hannun su, Yan Majalisun sun yaba da matakin da suka ce Datawan su suka dauka na kafa sabuwar PDP, inda suka gargadi hukumomin tsaron kasar da su kaucewa daukar duk wani mataki na musguna musu.
Yan Majalisun sun ce, akwai wasu da dama daga cikin su da yanzu haka basa cikin kasar, kuma da zaran sun dawo zasu bayyana goyan bayan su ga sabuwar PDP.
Rahotanni sun ce taron sasantawar da aka shirya yi tsakanin bangarorin Jam’iyar a ranar talata uku ga watan satumba na shekara ta 2013 bai yiwu ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.