Isa ga babban shafi
Nigeria

Nigeriya ba za ta daukaka kara kan Bakassi ba

Gwamnatin Nigeria tace ba zata daukaka kara ba, kan hukuncin kotun duniya, da ya baiwa kasar Cameroon, Yankin Bakassi mai dimbin arzikin mai.Wata sanarwa da Ministan shari’a, Mohammed Adoke ya sanyawa hannu daren jiya, tace gwamnatin Nigeria ta tattauna da masu bata shawara kan harkokin shari’a inda suka ki amincewa da yunkurin daukaka karar.Sanarwar tace, a halin yanzu da wa’adin daukaka karar ke karewa yau, gwamnatin bata da kwararan sabbin shaidu da zata iya gabatar wa, wadanda za su bata nasara, kuma gwamnatin ba zata kai karar da zata ji kunya a idan duniya ba.Sai dai a karshe, Gwamnatin tace zata ci gaba da kare ‘Yan kasar ta, a duk inda suke. 

Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan
Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.