Isa ga babban shafi

Ayyukan dan Adam sun haddasa bacewar rabin tsuntsayen Duniya- Rahoto

Wani rahoton kwararru da aka fitar a wannan mako, ya yi gargadin cewa, ayyukan dan Adam sun sanya kusan rabin adadin nau’ikan tsuntsayen duniya na raguwa, kuma akalla daya cikin takwas na tsuntsayen ke fuskantar barazanar karewa daga doron kasa.

Wasu nau'ikan tsuntsaye da ke kokarin bacewa a ban kasa.
Wasu nau'ikan tsuntsaye da ke kokarin bacewa a ban kasa. Ảnh : REUTERS/Sean Gardner
Talla

Rahoton da kungiyar “BirdLife International” ta saba fitarwa duk bayan shekaru hudu kan halin da tsuntsaye ke ciki a duniya, ya zo ne a daidai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ke jagorantar wani shiri na kasa da kasa don kare halittu da muhallin da suke ciki.

Rahoton ya ce yanzu haka adadin kashi 49 cikin 100 na nau'ikan tsuntsayen a duniya na raguwa, cikinsu kuwa har da ire-iren tsuntsayen da ba su saba fadawa cikin hatsarin fuskantar karewa daga doron kasa ba.

Masanan sun danganta halin da tsuntsayen ke ciki da matsaloli masu alaka ta kai tsaye da ayyukan dan Adam da suka hada da, sauyin tsare-tsaren gudanar da ayyukan noma, da sare dazuka, yawan farautar tsuntsayen da kuma Sauyin Yanayi.

BirdLife International, wacce ke adana bayanan bincike na shekaru masu yawa, ta ce a yanzu haka yawan nau’ikan tsuntsaye ya ragu da adadin akalla biliyan 2.9, a Arewacin Amurka, kwatankwacin kashi 29 cikin 100, idan aka kwatanta da adadin da ake da shi a shekarar 1970.

A yankin Turai kuwa, adadin nau’ikan tsuntsaye ya ragu ne da kusan miliyan 600, kwatankwacin kashi 18 cikin 100, daga shekarar 1980 zuwa yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.