Isa ga babban shafi

Pele da iyalansa sun gudanar da bikin Kirismeti a asibiti

Iyalan tsohon fitaccen dan wasan Brazil Pele, sun ziyarce shi a asibitin da yake jinya a Sao Paulo, inda yake karbar kulawar likitoci sakamakon ciwon daji, koda da kuma zuciya da yake fama da su, kamar yadda 'yarsa ta sanar a shafinta na sada zumunta.

Pele da iyalansa
Pele da iyalansa © Marca
Talla

A ranar Asabar ne 'dansa Edinho wanda a baya-bayan na aka bashi aikin horas da kungiyar Londaria da ke buga gasar Seria B, tare da 'yan 'uwansa mata wato Flavia da kuma Kely Nascimento suka ziyarci mahaifin nasu.

Kely ta wallafa wani hoton matar Pele Marcia Aoki da sauran 'yan 'uwanta da suka taru a asibitin da tsohon gwarzon dan kwallon duniyar yake jinya, duk da cewa basu wallafa hoton Pelen ba.

A ranar Laraba, asibitin da yake kwance ya fitar da sanarwar cewa Pele da kef ama da ciwon daji na hanji yana nuna sauki sosai, sai dai ana bashi kulawa akan ciwon koda da zuciya."

Daga bisani ne, 'ya'yansa mata suka sanar da cewa zai ci gaba da kasancewa a asibiti, inda a can ne zai gudanar da bikin Kirsimeti.

Pele ya lashe gasar cin kofin duniya a shekarar 1958 lokacin yana dan shekara 17, inda ya zura kwallaye uku a wasan dab da na kusa da karshe da kuma karin kwallaye biyu a wasan karsh.

Shi ne dan wasa daya tilo a tarihi da ya lashe gasar cin kofin duniya har uku, wato. ashekarun 1958, 1962 da 1970.

A cikin ‘yan shekarun nan, mutumin da ake yi wa lakabi da “Sarki a duniya kwallon kafa” ya fuskanci rashin lafiya, abin da ya sanya ba a cika ganinsa a wuraren taro da sauran bukukuwa ba.

An kwantar da shi a asibiti a ranar 29 ga watan Nuwamba bayan da likitoci suka ce yana bukatar kulawa sosai sakamakon ciwon daji, bayan tiyatar cire masa kari a hanjinsa a watan Satumban 2021.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.