Isa ga babban shafi

Pele: Shahararren dan wasan Brazil ya ce yana samun sauki

Shahararren dan wasan Brazil Pele ya ce yana cikin koshin lafiya, tare da fatan likitoci za su sallame shi cikin kankanin lokaci, yayin da yake jinya a wani asibiti da ke Sao Paulo.

Pele ya fara rashin lafiyar ne bayan ya halarci wani babban taro a birnin Paris na kasar Faransa
Pele ya fara rashin lafiyar ne bayan ya halarci wani babban taro a birnin Paris na kasar Faransa AFP/File
Talla

A wata sanarwa da ya fitar, ya ce sakonnin fatan samun sauki suna iso masa, daidai lokacin da yake ci gaba da kallon wasan Brazil a gasar cin kofin duniya.

Tun da farko hukumomin asibitin sun ce "har yanzu yana karbar kulawa, sannan bisa alamu yana samun sauki".

Hakan ya biyo bayan wani rahoto da aka fitar cewa jikinsa baya karbar maganin kona cutar daji da ake masa.

"Abokai na, ina so kowa ya ci gaba da kasancewa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, domin ina samun sauki yadda ya kamata," in ji Pele a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Instagram.

Pele mai shekaru 82 da haihuwa wanda ya lashe gasar cin kofin duniya sau uku yana kwance a asibiti tun ranar Talata, kuma a daren Alhamis ya fitar da sanarwar cewa ziyara ce da ya saba kaiwa likitoci a kowanne wata.

Tsohon gwarzon dan kwallon na duniya dai an yi masa tiyata ne wajen cire masa kari a hanjinsa cikin watan Satumbar 2021.

Sanarwar da Asibitin Isra'ila Albert Einstein ya fitar a ranar Asabar ta ce Pele yana ya samun kulawar likitoci bisa matsalar numfashi da ya samu.

Tuni magoya bayan tsohon dan kwallon na duniya suka fara aikewa da sakon jajjabi da fatan samun lafiya, daga sassa daban-daban na duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.