Isa ga babban shafi
Ebola

Masana sun tabbatar da ingancin sabon rigakafin Ebola

Hukumar lafiya ta duniya, WHO, ta ce mai yiwuwa ne sabon rigakafin cutar Ebola da masana suka samar ya zama karo na farko da aka cimma nasarar hakan. Inda hukumar ta ce a halin yanzu yawan maganin rigakafin da ake da shi ya kai dubu 300.

Cutar Ebola ta lakume rayuka a kasashen Afirka
Cutar Ebola ta lakume rayuka a kasashen Afirka KENZO TRIBOUILLARD / AFP
Talla

Idan har rigakafin cutar Ebolan ya samu amincewar masana kimiyya, za a fara amfani da shi a shekara ta 2018.

A wani gwaji da aka gudanar, a shakarar da ta gabata mutane 6,000 aka bai wa rigakafin a kasar Guinea, yayinda ake daf da shawo kan cutar, kuma a karshe babu wanda ya kamu da cutar.

A shakara ta 1976 aka fara gano cutar Ebola a Jamhuriyar Congo.

A shekara ta 2014 kuma cutar ta bazu daga kudancin kasar Guinea irin yadda ba a taba gani ba zuwa kasashen Saliyo da Liberia inda tayi sanadin mutuwar mutane 11,300.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.