Cutar Ebola Ta Sake Kashe Mutun Daya A Kasar Guinea.
An sake samun wani mutun daya da ya mutu a kasar Guinea sakamakon cutar Ebola wadda ta sake bulla a kasar.
Wallafawa ranar:
A ranar Lahadi data gabata aka sami mutun na farko daya mutu sakamakon wannan cuta bayan anyi bankwana da ita tun cikin shekarar data gabata.
Wani mai Magana da yawun Hukumomin lafiya a kasar Guinea, Ibrahima Sylla ya gaskata mutuwar mutun na biyu yau Talata.
Ya ce sun sami mutane takwas da suka mutu daga cikin mutane tara da suka kamu da wannan cuta.
A cewar sa mace ce ta gamu da ajalin ta a garin Nzerekore dake kan iyaka da kasar Liberia inda aka sami wasu da suka kamu da wannan cuta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu