Isa ga babban shafi
lafiya

Shirin kawar da kanjamau na samun kalubale

Majalisar dinkin duniya ta yi gargadi kan kalubalen da ake samu wajen kawar da cutar kanjamau nan da shekara ta 2030, yayin da ta koka kan yadda cutar ke ci gaba da yaduwa tsakanin manyan mutane bayan an yi nasarar rage yaduwarta tsakanin kananan yara.

Mutane miliyan 36.7 ke dauke da cutar kanjamau a duk fadin duniya amma akasarinsu na yankin Afrika da ke kudu da sahra
Mutane miliyan 36.7 ke dauke da cutar kanjamau a duk fadin duniya amma akasarinsu na yankin Afrika da ke kudu da sahra DR
Talla

A yayin da hukumar da ke yaki da cutar kanjamau ko kuma HIV ta majalisar ta fitar da wannan rahoton, ta kuma koka yadda cutar ke yaduwa tsakanin manyan mutane musamman a kasar Rasha, inda abin ya fi muni.

Ko daya ke rahoton ya bayyana cewa, an samu nasarar yakar cutar a cikin shekaru 20 da suka gabata musamman a tsakanin kananan yara amma hakan ya ci tura tsakanin manya.

Shugaban hukumar ta UNAIDS Michel Sidibe ya shaida wa taron manema labarai a birnin Geneva cewa, ya razana matuka saboda yadda cutar ta yi mummunar yaduwa tsakanin mayan cikin shekaru biyar.

Mr. Sidibe ya ce, matukar ba a farka ba, to lallai cutar ta Sida za ta sake yin barna wajen lakume rayuka da kuma haddasa asarar dukiyoyi.

Wata kididdiga ta nuna cewa, a halin yanzu akwai mutane kimanin miliyan 36.7 da ke dauke da cutar ta HIV a duk fadin duniya kuma akasarinsu na zaune a yakin Afrika da ke kudu da sahara.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.