Isa ga babban shafi
UNICEF

UNICEF ta bukaci a ci gaba da inganta rayuwar yara

Hukumar kula da ilimin kananan yara ta majalisar dinkin duniya UNICEF ta bukaci kasashen duniya su tashi tsaye don gina ci gaban da aka samu wajen inganta rayuwar yara kanana shekaru 25 da suka wuce wajen basu ilimi da kula da lafiyarsu.

Hukumar UNICEF a son kasashen duniya su ci gaba da inganta rayuwar kananan yara musamman ta fannin basu ilimi da kuma kula da lafiyarsu
Hukumar UNICEF a son kasashen duniya su ci gaba da inganta rayuwar kananan yara musamman ta fannin basu ilimi da kuma kula da lafiyarsu unicef.org
Talla

Rahotan da kungiyar ta UNICEF ta fitar a yau, mai taken "halin da yara kanana ke ciki a fadin duniya" ya ce an samu raguwar mutuwar yara kanana da kahsi 53 cikin 100 tun daga shekarar 1990 da kuma rage kamfen talauci.

Sai dai hukumar ta yi gargadin cewar, yara miliyan 69 da ke kasa da shekaru 5 ne za su iya mutuwa daga cututtukan da ake iya magance su kuma miliyan 167 na iya fuskantar talauci a shekaru 15 masu zuwa muddin ba a dauki mataki ba.

Rahotan ya yi hasashen cewar za a aurar da mata da 'yan mata miliyan 750 nan da shekarar 2030, shekarar da majalisar dinkin duniya ta gindaya a matsayin lokacin kammala sabon shirinta na cimma wasu muradun ci gaba.

Hukumar ta bayyana cewar, a kudancin Asia da Afrika Kudu da sahara, ana samun haihuwa daga iyayen da basu da ilimi, kuma hakan kan haifar da yawan mace mace sabanin na iyayen da suka samu ilimin Sakandare.

Rahotan ya kuma ce yanzu haka yara miliyan 124 basa zuwa makaranta.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.