Isa ga babban shafi

Mahara sun kashe direbobi goma a kusa da iyakar Mexico da Amurka

Akalla mutane 10 ne suka mutu sannan wasu tara suka jikkata a jiya Asabar bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan ayarin direbobin da ke gudanar da rangadi a garin Ensenada da ke arewacin kasar Mexico, kusa da kan iyaka da Amurka, kamar yadda hukumomi suka bayyana. 

Kwambar motoci daga Mexico a daidai kan iyakar kasar da Amurka.
Kwambar motoci daga Mexico a daidai kan iyakar kasar da Amurka. REUTERS - JOSE LUIS GONZALEZ
Talla

Direbobin sun tsaya ne a gefen babbar hanya, yayin da wasu gungun mutane suka fito daga cikin wata motar akori-kura sannan suka bude musu wuta. 

Sanarwar da hukumomin yankin suka fitar ta ce, ofishin mai gabatar da kara na jahar Baja California, inda garin Ensenada ya ke, wanda kuma ya ke fama da ta'addancin masu safarar miyagun kwayoyi, ya sanar da kafa kwamiti na musamman domin gano wadanda suka aikata laifin da kuma gano musabbabin hakan da suka yi. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.