Isa ga babban shafi

Fadar White House ta yi tir da kisan wasu Amurkawa hudu a Mexico

Fadar White House ta yi tir da garkuwa da aka yi da 'yan asalin Amurka hudu a Mexico, wadanda aka tsinci gawarsu yashe a gefen hanya.

Shugaban Amurka Joe Biden kenan tare da takwaransa na Mexico Andres Maneul Lopez Obrador yayin wani taron shugabannin kudanccin Amurka ranar 09, ga watan Janairun 2023
Shugaban Amurka Joe Biden kenan tare da takwaransa na Mexico Andres Maneul Lopez Obrador yayin wani taron shugabannin kudanccin Amurka ranar 09, ga watan Janairun 2023 REUTERS - HENRY ROMERO
Talla

Gwamnatin Amurka ta ce shakka babu za a dauki matakin gaggawa na shari’a kan wadanda suka aikata wannan mummunan aiki.

“Za mu yi aiki tare da gwamnatin Mexico, domin tabbatar da cewa doka ta yi aiki yadda ya kamata a kan wannan danyen aiki,” in ji mashawarcin tsaron Amurka John Kirby.

Amurka ta ce shakka babu ba za ta yi kasa a gwiwa ba, har sai ta tabbatar da cewa ta kwato wa 'yan kasarta hakkokinsu, da kuma tabbatar da cewa an hukunta wadanda aka samu da hannu da aikata kisan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.